Nijeriya za ta biya bashin dala biliyan 3.5 ga Chana a shekarar 2047

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Daga shekarar 2023, gwamnatin tarayya, a ƙarƙashin zaɓaɓɓun shugabannin ƙasa bakwai da za a yi a gaba, za ta ɗauki sama da shekaru 24 tana biyan bashin dala biliyan 3,593.42 da Nijeriya ta ciwo daga bankin Exim na ƙasar Sin a halin yanzu.

Sai dai kuma, hakan zai yiwu ne kawai idan har Nijeriya ba ta sake karɓar wani lamuni daga ƙasashen Asiya ba kafin ƙarshen wa’adin mulkin wannan gwamnati da kuma wasu na gabanta.

Fwamnatoci biyar da za a yi:

Gwamnatocin da za su fara mulki daga 2023, 2027, 2031, 2035, 2039, 2043, da kuma wataƙila gwamnatin shekarar 2047 za su ɗauki nauyin samar da kuɗaɗe don aiwatar da manyan ayyuka, waɗanda idan an kammala su yadda ya kamata, ya kamata su samar da isassun kayan kuɗi na biyan ba wai kawai bashin ba amma har da lamuni da kuma samar da ayyuka don inganta zamantakewa da tattalin arzikin Nijeriya da ‘yan Nijeriya.

Jimlar bayanan bashin:

Adadin bashin da ake bin Nijeriya a halin yanzu ya kasu kashi biyar, wato: Multi-lateral Group, World Bank Group, Bilateral, Business and Promissory Notes. Dangane da bayanin basukan watan Satumba da Ofishin Kula da Bashi (DMO) ya fitar, an sanya jimlar a kan dala biliyan 3,469.45, jimla ta gaba kuma mafi girman basukan da bankin duniya ke bin ƙasar shi ne dala miliyan 18,284.09, adadin da ya kai kashi 48.17.

Me yasa lamunin Chana?

Da ta ke ƙarin haske kan dalilan da suka sa Nijeriya ta kasance gida da rancen ƙasar Sin a wani taron manema labarai a bara, ministar kuɗi, kasafi da tsare-tsaren ƙasa, Zainab Ahmed, ta ce, hakan ya faru ne saboda bankin duniya da bankin raya Afirka (AfDB) sun ƙasa nuna sha’awarsu ga Nijeriya, musamman kafin da kuma lokacin koma bayan tattalin arziki a shekarar 2016.

Shi ma da yake magana a ɗaya ɓangaren, Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan, ya ce, hakan ya zama dole saboda tsananin buƙatar samar da ababen more rayuwa da kuma ƙarancin isassun kuɗaɗe da ake da su, wanda ya biyo bayan matsalar ƙarancin mai tsakanin 2014 zuwa 2016 da kuma faɗuwar farashin ɗanyen mai a Nijeriya, babban tushen samu kuɗaɗe ga ƙasar.

Ya ce, ta haka ne kawai za a iya samar da kuɗaɗen da ake buƙata don gudanar da manyan ayyukan cigaban tattalin arziki.

Wata ƙwararriya kan harkokin haraji kuma wacce ta kafa gidauniyar Sana’a da Ilimi, Amina Ado, ta ce, Nijeriya ta zaɓi wannan lamuni ne saboda sauƙin kuɗin ruwa na rancen bankin Exim na Chana idan aka kwatanta da rancen kasuwanci da ake samu daga kasuwannin babban birnin ƙasar.

Ayyukan da aka saka akan lamunin:

  1. Aikin Sadarwa na tauraron Ɗan Adam a Nijeriya
  2. Tsarin Sadarwa na Tsaron Jama’a na Nijeriya
  3. Aikin sabunta layin dogo na Nijeriya (sashen Idu – Kaduna)
  4. Aikin Jirgin Ƙasa na Abuja
  5. Aikin Cibiyar Fasahar Sadarwa
  6. Aikin Faɗaɗa Tashoshin Jiragen Saman Nijeriya (Abuja, Kano, Legas da Fatakwal)
  7. Aikin samar da wutar lantarki na Zungeru na Nijeriya
  8. Aikin Shuka – Tsarin Shinkafa 40 na Nijeriya da dai sauransu.
  9. Aikin sabunta layin dogo na Nijeriya (ɓangaren Legas – Ibadan)
  10. Gyara da inganta aikin titin Abuja – Keffi – Markurdi.
  11. Samar da Hannun Jari da Kayayyaki na Aikin Jiragen Ruwa na Abuja.
  12. Aikin Samar Da Ruwa a Abuja
  13. Aikin Faɗaɗa Tashar Jiragen Sama Na Nijeriya Huɗu.

Daga cikin waɗannan, wataƙila aikin sabunta layin dogo na Nijeriya (sashen Idu-Kaduna), aikin layin dogo na Abuja, aikin sabunta layin dogo na Nijeriya (sashen Legas-Ibadan), aikin faɗaɗa tashoshin jiragen sama na Nijeriya huɗu (Abuja, Kano, Legas da Fatakwal), da gyare-gyare da inganta aikin hanyar Abuja-Keffi-Makurdi, ya nuna bajintar ƙasar.

Barazana ga kadarorin ƙasa:

Dangane da barazanar da ƙasar Sin za ta iya ɗauka na karɓe kadarorin ƙasa idan Nijeriya ta gaza biya, shugabar hukumar ta DMO, Oniha ta ce, akwai yarjejeniyar lamuni da mai ba da lamuni da mai amsar lamuni suke kiyayewa sosai.

Ta ce, “yarjejeniyar lamuni ta tanadi cewa idan aka samu saɓani a tsakanin ɓangarorin, matakin farko shi ne ɓangarorin su warware a cikin kansu, idan kuma hakan ya gaza, sai su tafi a yi sulhu. A takaice dai, mai ba da lamuni, a wannan yanayin, ƙasar Sin ba za ta mallaki wata kadara ba a farkon alamar taƙaddama gami da gazawa.”