Nijeriya za ta faɗa cikin matsalar abinci a 2023, inji IMF

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Asusun Lamuni na Duniya IMF, ya ce Nijeriya na fuskantar barazanar faɗawa cikin matsalar abinci a 2023, saboda hauhawar farashi da kuma ambaliyar ruwa da ta ɗaiɗaita amfani gona da tsadar taki.

A cewar ƙiddidigar hukumar NBS, hauhawar farashi a Nijeriya ya kai maki 23.72 cikin 100 a watan Oktoban 2022, yayin da farashin wasu kayayyakin abinci ya ƙaru daga kashi 50 zuwa 100.

IMF ta ce la’akari da wannan yanayi da ake ciki, farashin kayan abinci zai munana a 2023.

Sannan rahoton IMF ya ce duk da irin waɗannan matsaloli, akwai kuma yaƙin Ukraine da ke shafar tattalin arziki da farashin kayan abinci.

IMF ta ce muddin ba a tashi tsaye da bijiro da matakai ba, ‘yan Nijeriya da dama za su rasa abinci ko damar iya ciyar da kansu nan gaba kaɗan.

A makon da ya gabata ne Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa a Nijeriya ta ce ‘yan ƙasar miliyan 133 ke cikin talauci, kuma galibinsu ba sa samun ilimi da tsaro da kulawar lafiya.