Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai halarci taron haɗin-gwiwa na ƙasashen Larabawa da Musulunci da za a gudanar a Birnin Riyadh dake Saudiyya don tattauna batutuwan da suka shafi Gabas ta Tsakiya.
Shugaba Tinubu zai jadada goyon bayan Nijeriya ne kan ƴancin Falasɗinawa a taron wanda ya samu gayyatarsa daga Yarima, Mohammed Bin Salman daga Saudiyya.
Daga cikin ƴan tawagar shugaban ƙasa akwai manyan jami’an gwamnati da suka haɗa da; Ministan Harkokin wajen ƙasar, Ambasada Yusuf Tuggar; Mai ba shugaban ƙasa shawara kan Harkokin Tsaro, Mallam Nuhu Ribaɗu; Ministan yaɗa Labarai da Wayar da kan al’umma, Alhaji Mohammed Idris; da Darakta-Janar na Hukumar Leken Asiri ta Ƙasa (NIA), Amb. Mohammed Mohammed.