Nijeriya za ta karɓi rigakafin korona samfurin Johnson & Johnson guda milyan 29.8

Daga WAKILINMU

Gwamnatin Nijeriya na sa ran ta karɓi allurar rigakafin cutar korona samfurin Johnson & Johnson (J&J) ƙwara milyan 29.8, kamar yadda Dr Faisal Shuaib ya bayyana a Litinin da ta gabata.

Shuaib wanda shi ne Daraktan Hukumar Bunƙasa Lafiya a Matakin Farko ta Ƙasa (NPHCDA), ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai na mako-mako da aka saba gudanarwa game da sha’anin yaƙi da cutar korona a Abuja.

Ya ce gwamnati ta sanya hannun karɓar rigakafin ne ta Ƙungiyar Ƙasashen Afirka (AU), sannan maganin zai shiga hannu ta shirin COVAX ya zuwa ƙarshen Mayu ko farkon Yuni.

Jami’in ya ce kafin shigowar sabon rigakafin, Nijeriya ta kammala yi wa ‘yan ƙasa rigakafin AstraZeneca zagaye na biyu ga waɗanda suka samu zarafin yin na farkon.

Ya ce Hukumar Tantance Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) na ci gaba da tattaunawa da kamfanin sarrafa maganin domin gudanar da bincike kan magungunan nasu.

A cewar Shuaib ya zuwa 26 ga Afrilu, an yi wa ‘yan Nijeriya su 1,173, 869, kwatankwacin kashi 58.3 cikin 100 na adadin ‘yan ƙasa, rigakafin AstraZeneca wanda hakan ya yi daidai da burin gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *