Nijeriya za ta karɓi rigakafin korona milyan 3.92 a Agusta – Gwamnati

Daga AISHA ASAS

Ana sa ran Nijeriya ta karɓi ƙarin aullurar rigakafin korona na Oxford/AstraZeneca guda milyan 3.92 ya zuwa farkon Agusta.

Shugaban Hukumar Bunƙasa Lafiya a Matakin Farko, Dr Faisal Shuaib ne ya bayyana haka a Talatar da ta gabata a Abuja. Sai dai bai bayyana takamammiyar ranar da maganin zai shiga hannun Nijeriya ba.

Ya ce, “Mun samu labarin Nijeriya za ta samu rigakafin korona na Oxford/AstraZeneca guda milyan 3.92 ya zuwa ƙarshen Yuli ko farkon Agusta.”

Ya ƙara da cewa, “Idan muka samu ƙarin bayanai game da takamammiyar ranar da za a karɓi maganin, za mu bayyana komai.”

Shuaiba ya ce sun gudanar da taron jin ra’ayoyin jama’a a shiyyar Arewa ta tsakiya da kuma Arewa-maso-gabas game da sha’anin cutar korona.

Ya ce yayin da Kwamitin Shugaban Ƙasa Kan Yaƙi da Cutar Korona ke ci gaba da ƙoƙarinsa wajen aiwatar da ayyukan da suka rataya a kansa, kwamitin zai gudanar da taron da ya shirya don ganawa da masu ruwa da tsaki da sauran al’ummar yankin Kudu-maso-kudu kan batun rigakafin cutar korona.