Nijeriya za ta ƙirƙro rigakafin korona ba da daɗewa ba, cewar Minista Onu

Daga BASHIR ISAH

Ministan Kimiyya da Fasaha Ogbonnaya Onu, ya ce nan ba da daɗewa ba Nijeriya za ta ƙirƙiro maganin rigakafin cutar korona don amfanin ‘yan ƙasa.

Ministan ya ce hakan zai samu ne ta dalilin tawagar ƙwararrun kimiyya da aka kafa ƙarkashin jagorancin Dr Oladipo kolawole na Jami’ar Adeleke, inda tawagar ke kan gudanar da bincikenta kan maganin cutar korona.

Onu ya bayyana haka ne a Abuja a lokacin da ya karɓi baƙuncin wani kwamitin masana kimiyya a Abuja.

Ministan ya yaba wa tawagar masu binciken daga Jami’ar Adeleke bisa sanya sunan Nijeriya a jerin ƙasashen duniya masu ƙoƙarin ƙirƙiro maganin rigakafin korona.

Yana mai cewa samar da magani ta cikin gida zai taimaka wa Nijeriya wajen iya kula da ƙalubalan da suka dabaibaye ta.

A cewarsa, “Nijeriya ba za ta ci gaba da dogaro da rigakafin da wasu ƙasashe ke ƙirƙirowa ba kasancewar a wannan zamani kowace ƙasa ƙoƙari take ta ga ta iya ƙirƙira wa kanta magungunan da za ta riƙa amfani da su.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *