Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya NIMET da takwararta ta NIHSA da ke hasashen zubar ruwan sama, sun yi gargaɗi kan yiwuwar fuskantar matsananciyar ambaliyar ruwa a jihohin shiyyar Arewa ta Tsakiya da Kudu maso Yammacin qasar nan da kwanaki ƙalilan masu zuwa.
Darakta Janar na hukumar NIMET, Farfesa Mansur Bako Matazu ya ce hasashensu ya nuna yiwuwar samun mamakon ruwan sama a yankunan 2 wanda zai zama ƙari kan ɓallewar wasu madatsun ruwan ƙasar, lamarin da zai haifar da gagarumar ambaliya.
Hasashen hukumomin biyu na zuwa ne a daidai lokacin da jihohin Benuwai da Kogi ke tsaka da fuskantar mummunar ambaliyar ruwan da ta haddasa asarar rayukan jama’a da kuma ɗimbin dukiya, ambaliyar da bayanai ke cewa ita ce mafi muni da ƙasar ta gani tun bayan makamanciyarta a shekarar 2012.
Farfesa Bako Matazu ya ce tun a watan Fabrairun da ya gabata suka yi hasashen samun ambaliyar ruwa a sassan ƙasar, sannan kuma suna tunasar da al’umma halin da ake ciki a sanarwar hasashen yanayin da su ke fitarwa a kowanne wata.
Farfesa Matazu ya ce a shekaru masu zuwa za a samu ruwan sama mai yawan gaske, wanda hakan ke cikin matsalolin sauyin yanayin da aka fuskanta.
A daminar bana dai, jihohin Nijeriya 29 daga cikin 36 da ƙasar ke da su ne suka fuskanci ambaliyar ruwa, wadda kuma ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da lalata dukiyar miliyoyin naira musamman a jihohin Arewacin ƙasar da suka ƙunshi Taraba da Jigawa da Kogi da kuma Jihar Kano.