NLC a Neja ta ƙi amincewa da tallafin N110m da gwamnatin jihar ta ware mata

Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) reshen Jihar Neja, ta ƙi amincewa da tallafin kuɗi Naira miliyan 110 da gwamnatin jihar ta ware mata, tana mai cewa a ƙara kuɗin cikin tallafin da gwamnati ta tanadar wa ma’aikatan jihar.

Shugaban NLC na jihar, Comrade Abdulkarim Idris Lafene, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai ranar Litinin a Minna, babban birnin jihar.

Lafene ya nuna ɓacin ran ƙungiyar ga gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Umar Bago saboda cire masu karɓar fansho daga tsarin rabon tallafin, lamarin da NLC ta ce bai zai saɓu ba.

Shugaban ƙungiyar ya umarci ma’aikatan gwamnatin jihar da su ƙaurace wa kwamitin rabon tallafin da gwamnatin jihar ta kafa.

Kazalika, ya jaddada cewa shirin fara yajin aikin gargaɗi na yini biyu da NLC ta ƙuduri aniyar farawa a ranar Talata, yana nan daram.

Haka nan, ya ce buƙatar ƙungiyar a jihar shi ne gwamnati ta yi wa ɗaukacin ma’aikatanta ƙarin albashi na N50,000 ga kowa a matsayin tallafin rage raɗaɗin ƙuncin rayuwa har na tsawon wata shida.

“Naira miliyan 110 da Gwamnatin Neja ta ware wa NLC a matsayin tallafi, a yi amfani da kuɗin wajen yi wa ma’aikatan jihar da masu karbar fansho a matakin jiha da ƙananan hukumomi ƙarin albashi,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *