NLC ta dakatar da ƙudirin tafiya yajin aiki – Fadar Shugaban Ƙasa

Daga BASHIR ISAH

Fadar Shugaban Ƙasa ta ce Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) da ta ‘yan Kasuwa (TUC) sun amice da su dakatar da ci gaba zanga-zangar da suka fara.

Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Mista Dele Alake, shi ne ya bayyana haka cikin sanarwar da ya fitar a Abuja.

Ya ce an cim ma hakan ne biyo bayan tattauna da ƙungiyoyin suka yi da Shugaba Tinubu inda suka nuna gamsuwarsu dangane da tabbacin da Shugaban ya ba su na cim ma buƙatunsu.

Yayin tattaunawar, Comrade Joe Ajaero ne ya jagoranci ɓangaren NLC, yayin da Comrade Festus Usifo ya jagoranci TUC.

Taron shi ne irin sa na farko da Tinubu ya yi da NLC tun bayan da ƙungiyar ta ƙuduri aniyar tafiya yajin aiki sakamakon cire tallafin mai.

Manhaja ta rawaito a ranar Laraba mambobin NLC suka gudanar da zanga-zangar gama gari da zummar cim ma buƙatunsu a wajen gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *