NLC ta gargaɗi Buhari kan yinƙurin ƙwace lasisin ASUU

Daga WAKILINMU

Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC), ta gargaɗi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari kan take-taken neman ƙwace lasisin rijistar Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) saboda rashin miƙa bayanan hada-hadar kuɗaɗenta na tsawon shekaru biyar.

NLC ta yi wannan gargaɗi ne a matsayin martani ga wani rahoton da ya nuna Gwamnatin Tarayya na shirin janye rijistar ASUU saboda saɓa ƙa’ida, inda ta aike da wasiƙar gargaɗin zuwa ga Ministan Ƙwadago, Chris Ngige da Shuganan NLC ma Ƙasa, Ayuba Wabba.

NLC ta yi tsayin daka kan cewa, lallai ASUU ta miƙa rahoton hada-hadar kuɗaɗenta baki ɗaya har zuwa 2021, don haka ba ta ga dalilin da zai sa gwamantin yin tunanin ɗaukar wannan mataki a kanta ba.

A cewar NLC, cikin rahoton da ta miƙa wa gwamnati, ASUU ta ce ba a bin ta bashin rahoton hada-hadar kuɗaɗen da ta yi daga 2014 zuwa 2021.

NLC ta ce ta fahimci jinkirin da ASUU ta yi wajen miƙa wasu daga rahotannin hakan ya faru ne saboda ɓullar annobar Korona.

Haka nan, ta ce duk da ƙalubalen annobar Korona ɗin, ta gano ASUU ta iya biyan harajin da ke kanta ga gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *