NLC ta umarci mambobinta su tafi yajin aiki kan rashin biyan mafi ƙarancin albashi

Daga USMAN KAROFI

Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ta bayar da umarnin yajin aikin sai baba ta gani a duk jihohin da har yanzu ba su fara aiwatar da sabon albashi ba, daga ranar 1 ga watan Disamba, 2024. Wannan umarni yana cikin matsayar da ƙungiyar ta cimma a taron majalisar gudanarwa na ƙungiyar(NEC) da suka yi a ƙarshen mako. A cewar ƙungiyar, rashin bin doka da jinkirin aiwatar da sabon albashi ya zama abin damuwa ga ma’aikata da ke fama da tsadar rayuwa mai tsanani.

Ƙungiyar ta NEC ta bayyana cewa, wannan gazawa da wasu gwamnatocin jihohi suka yi na rashin bin doka wajen aiwatar da albashi, yana nuna rashin adalci da rashin tausayawa ga ma’aikatan da ke fama da raɗaɗin tattalin arzikin ƙasar nan. NLC ta kuma ce ba za ta zuba ido tana kallo a ci gaba da tauye haƙƙoƙin ma’aikata ba. Ƙungiyar ta umarci dukkan jihohin da ba su fara aiwatar da sabon albashi ba su fara yajin aiki a ranar 1 ga Disamba, har sai an biya musu buƙatunsu na albashin ma’aikata.

Haka kuma, NLC ta sanar da kafa wani kwamitin tabbatar da aiwatar da albashi a matakin Ƙasa wanda zai gudanar da gwajin jin ra’ayin ma’aikata da wayar da kan ‘yan ƙasa game da muhimmancin samun adalci ga ma’aikata. Kwamitin zai shirya tarurruka don ƙarfafa gwiwar ma’aikata da sauran jama’a wajen tunkarar wannan ƙalubale na rashin biyan albashi. Ƙungiyar ta ce ba za ta yi ƙasa a guiwa ba wajen ɗaukar matakin da ya dace domin tabbatar da aiwatar da sabon albashi a faɗin ƙasar nan.

A wani ɓangare, NLC ta zargi masu sayar da man fetur da ƙara farashin man fetur fiye da yadda yake a kasuwar duniya. Ƙungiyar ta ce ana amfani da wannan damar wajen wahalar da al’umma musamman ma’aikata da ke fama da tsadar rayuwa. Ƙungiyar ta NLC ta nuna damuwa ga abin da ta kira dabarun da ake amfani da su wajen karin farashi da kuma rashin samun sassaucin farashi duk da cewa ƙasar na da hanyoyin magance haka.

Ƙungiyar ta ƙara da cewa, tana kira ga gwamnati da ta gaggauta dawo da matatun mai na cikin gida a Fatakwal, Warri da Kaduna domin rage ƙarfin kamfanonin da ke da iko da kasuwar mai a ƙasar. Haka zalika, NLC ta yi kira ga gwamnati da ta samar da tsare-tsare na rage raɗaɗin tattalin arziki ga ‘yan Nijeriya, kamar samar da kiwon lafiya mai sauƙi da tsare-tsaren da za su rage talauci tare da tsarin albashi da ya dace da tsadar rayuwa.