NNPC da Ɗangote sun ƙulla yarjejeniyar bunƙasa gas don takin zamani

Daga AMINA YUSUF ALI

Kamfanin rarraba man fetur na Nijeriya, NNPC, ta bayyana cewa, ta ƙulla yarjejeniya tare da kamfanin attajiri Ɗangote don ta dinga samar musu da gas. 

Kamfanin NNPC, ya bayyana cewa, ɓangarorin biyu sun rattaba hannu a yarjejeniyar ne  A garin Abuja yayin taron a kan harkar makamashi na ƙasa karo na biyar. Wanda aka gudanar ranar Alhamis 3 ga watan Maris, 2022.

Ɓangarorin da suka qulla yarjejeniya a tsakaninsu sun haɗa da, NNPC, Kamfanin Shell (SPDC), Kamfanin Gas na Total(GACN).

Da ya ke faɗar albarkacin bakinsa game da  yarjejeniyar, Mele Kyari, shugaban Kamfanin NNPC ya bayyana cewa, wannan wani hovvasa ne daga gwamnati don bunqasa sarrafa gas ɗin. 

 Sannan kuma wannan wani yunƙuri ne daga Gwamnati don bunƙasa harkar samar da takin zamani a ƙasar. Hakan kuma yana daga cikin muradanta ta ga ƙasar ta dogara da kanta wajen samar da gas ɗin. 

A cewar sa, NNPC tana farin ciki da ƙulla wannan yarjejeniya da Ɗangoten. Domin da ma kafin haka, shi ne yake samar da kaso 65 na takin zamanin da ake amfani da shi a ƙasar. 

Shi ma Aliko Ɗangote shugaban rukunin kamfanoni na Aliko Group, ya bayyana cewa, wannan alaƙar za ta sa ƙasar nan ta samu rarar kuɗaɗen da take kashewa ta hanyar shigo da takin daga ƙasashen waje.