NNPC ya bayyana gidajen man da suka shigo da gurɓataccen mai daga Belgium

*Lamarin ya rutsa da Oando, MRS, AY Maikifi da Duke Oil

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Babban Manajin Darakta Kamfanin Man Fetur (NNPC), Malam Mele Kyari, ya bayyana yadda aka shigo da gurɓataccen man fetur mai sinadarin ‘Methanol’ fiye da kima daga Ƙasar Belgium ba tare da an gano shi ba da kuma kamfanonin man da suka shigo da shi.

Wannan na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan Ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva, ya nuna cewa, gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin gudanar da wani gagarumin bincike domin bankaɗo al’amuran da suka shafi shigo da kayayyaki da kuma tantance gurɓatattun kayayyaki.

Babban Manajin Darakta na Kamfanin NNPC, Mele Kyari ne ya bayyana haka a ranar Laraba, 9 ga watan Fabrairu, 2022, yayin wani taron tattaunawa da daddare a Abuja, inda ya yi bayani kan matsalar da ta haifar da ƙarancin mai da kuma ɓullar layukan mai a Abuja, Legas, da wasu jihohi da dama.

Kyari ya bayyana cewa, wasu ’yan kasuwa 4 ne masu shigo da man daga Antwerp da ke ƙasar Belgium, inda jami’ai masu tantance ingancin kayayyaki suka kasa gano yawan sinadarin Methanol da ke cikinsa, na farko a wajen shigo da shi ƙasar Belgium sannan kuma a lokacin da ya isa Nijeriya.

Shugaban kamfanin na NNPC wanda bai bayar da ranar da za a shigo da su Nijeriya ba, ya bayyana cewa, a ƙarshen watan Junairu ne hukumar NNPC ta gano lamarin, biyo bayan rahoton da aka samu daga jami’ansu kan kasancewar wasu kwayoyin ‘emulsion’ a cikin kayayyakin man fetur ɗin da aka aika zuwa Nijeriya daga Antwerp-Belgium.

Ya ce, binciken da NNPC ya yi ya nuna akwai sinadarin Methanol a cikin wasu kayayyaki 4 na fetur da kamfanonin mai na MRS, Emadeb/Hyde/AY Maikifi/Brittania-U Consortium, Oando da Duke Oil suka shigo da su.

MRS ta yi amfani da jirgin MT Bow Pioneer; Emadeb/Hyde/AY Maikifi/Brittaniya-U Consortium ta shigo da samfurin ta jirgin ruwan MT Tom Hilde, inda Oando ta yi amfani da jirgin MT Elka Apollon, yayin da Duke Oil ya shigo da fetur ɗinsa ta hanyar amfani da MT Nord Gainer.

Ya kuma ce, masu binciken ingancin NNPC da suka haɗa da GMO, SGS, GeoChem da G&G da kuma jami’an binciken da Hukumar Kula da Man Fetur ta ‘Midstream da Downstream’ ta naɗa sun tabbatar da cewa kayan sun cika ƙa’idojin Nijeriya.

’Yan Nijeriya na da shakku kan binciken shigo da gurɓataccen mai a ƙasar:

A wani lamarin kuma, masu ruwa da tsaki a Nijeriya sun fara tsokaci ga ikirarin gwamnatin Nijeriya na cewa za ta gudanar da gagarumin bincike kan batun shigar da gurɓataccen man fetur daga ƙetare zuwa cikin ƙasar.

A ranar Laraba rahotanni suka ambato ƙaramin ministan mai, Timipre Sylva na cewa, za a yi bincike don bankaɗo dalilin shigar da gurɓataccen man a Nijeriya.

Masu motoci da yawa ne suka koka a kan lalacewar ababen hawansu, bayan sun sha man fetur ɗin mai yawan sinadarin methanol fiye da kima.

Kafofin yaɗa labaran Nijeriya sun ambato ƙaramin ministan fetur jim kaɗan bayan taron majalisar zartarwar ƙasar na cewa gwamnati ta tashi haiƙan wajen tunkarar batun gurɓataccen man fetur ɗin da ya cika gidajen mai.

Ministan ya kuma nemi ’yan ƙasar su ƙara haƙuri har gwamnati ta kammala bincike kafin a fara batun bayyana sunayen masu hannu.

Rahotanni sun kuma ambato shi yana cewa kafin yanzu babu wanda ke duba adadin methanol a cikin man fetur ɗin da ake shiga da shi ƙasar.

Lamarin da ya sa wasu ke tambayar da ma ƙasar ba ta da sashen tantance ingancin man da ake shigarwa daga waje.