Daga BELLO A. BABAJI
Kimanin sati uku kenan da Kamfanin Man fetur na Ƙasa, NNPCL ya ƙara kuɗin litar fetur wanda ya sa gidajen man dake ƙarƙashinsa suka sauya farashinsu daga N998 a zuwa N1,025 a Legas.
Gidajen man da ke ƙarƙashin kamfanin kai-tsaye na sayarwa akan N,1025 yayin da waɗanda ke mallakar ƴan kasuwa ne ke sayarwa akan N1,100.
Haka ma Abuja, kamfanin na sayarwa akan N1,060 daga N1,030 na kowacce lita tun daga ranar Talata.
Tun daga lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur a Nijeriya ne, farashinsa yake ta hauhawa wanda daga N184 ya kai har zuwa N1,025.
Kawo yanzu dai babu wani jawabi na musamman daga NNPCL kan dalilin ƙaruwar farashin. Tun lokacin da NNPCL ya fara dakon mai daga matatar Ɗangote ne a wata Satumba, aka sake samun ƙarin farashin.
Matatar Ɗangote dai ta musanta batun sayarwa NNPCL lita akan N898 da ya yi ikirari a farko inda ya ƙalubalanci matatar ta faɗi yadda ta sayar masa.
Daga baya, kamfanin man ya fitar da jaddawalin yadda farashinsa zai kasance a jihohin Nijeriya.