NNPC zai fara gyaran matatar mai ta Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA

Gwamnatin Nijeriya ta amince ta ƙulla yarjejeniya da wani kamfani a Koriya ta Kudu da zimmar gyara matatar man fetur ta Kaduna da ke Arewacin ƙasar.

Shugaban kamfanin mai na Nijeriya NNPC, Mele Kyari, shi ne ya saka hannu a madadin Nijeriya yayin taro kan harkokin lafiya da tawagar ƙasar ke halarta a Koriya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari.

Sanarwar da NNPC ya wallafa a shafinsa na Tiwita ta ce nan gaba kaɗan za a fara zagayen duba gyaran da za a yi.

A ƙarshen shekarar 2021 ne gwamnatin Nijeriya ta ware fiye da Dala biliyan ɗaya don gyara matatar mai da ke birnin Fatakwal, aikin da ta ce ana ci gaba da yi.

Kazalika, za a ci gaba da irin wannan aiki a matatar ta garin Warri na Jihar Delta.