NNPP ta buƙaci INEC ta dakatar da shirin Kwankwasiyya na yi wa jam’iyyar kwaskwarima

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Jam’iyyar NNPP ta rubutawa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), inda ta buƙaci hukumar ta dakatar da shirin da wasu ƙungiyoyi ke yi na sauya tambarin jam’iyyar.

Jam’iyyar ta kuma rubuta wa Sanata Rabiu Kwankwaso, ɗan takararta na shugaban ƙasa a 2023, domin ya kawo ƙarshen yarjejeniyar da ta shigar da ƙungiyar Kwankwasiyya cikin al’amuran jam’iyyar a zaɓen 2023.

Wasiqun da Peter Ogah, lauyan jam’iyyar ne ya rubuta wa INEC da Kwankwaso ya sanya wa hannu kuma aka miƙa wa manema labarai ranar Laraba a Legas.

Wasiƙar zuwa ga INEC tana ɗauke da taken: “Shirye-shiryen da ba su da izini na canja tambarin NNPP da kuma yi wa Kundin Tsarin Mulkin jam’iyyar kwaskwarima.”

Idan za a iya tunawa, a ranar 5 ga watan Satumba ne wani ɓangare na jam’iyyar a ƙarƙashin jagorancin Manjo Agbo ya kori ɗan takarar shugaban ƙasa, Rabi’u Musa Kwankwaso, bisa zarginsa na cin hanci da rashawa da kuma karkatar da kuɗaɗen yaƙin neman zaɓen jam’iyyar.

Ogah ya sanar da INEC a cikin wasiƙar cewa wanda yake karewa ya sanar da kamfanin wani labari cewa wasu mutane na ɗaukar matakin sauya tambarin jam’iyyar tare da gyara Kundin Tsarin Mulkin ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *