Kwamitin Amintattu (BoT) na Jam’iyyar NNPP ya dakatar da ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar a babban zaɓen da ya gabata, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, bisa zargin yi wa jam’iyyar zagon-ƙasa.
Kazalika, Kwamitin (BoT) ya dakatar da Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) na jam’iyyar.
Har wa yau, Kwamitin ya naɗa shugabannin jam’iyyar a matakin ƙasa ƙarƙashin jagorancin Dr Agbo Major a matsayin shugaban riƙo na ƙasa da kuma Mr Ogini Olaposi a matsayin muƙaddashin Sakatsren jam’iyya na ƙasa tare da wasu mutum 18.
Jaridar News Point Nigeria ta kalato cewar, dakatarwar ta wata shida ne.
Majiyarmu ta ce an cim ma wannan matsaya ne a wajen babban taro na musamman da jam’iyyar ta gudanar a Rockview Hotels da ke Apapa, Jihar Legas.
A ranar Alhamis da ta gabata NWC ya bada sanarwar dakatar da mu’assasin jam’iyyar ta NNPP, Dr Boniface Aniebonam da Sakataren yaɗa labarai na ƙasa, Major.
Sa’ilin da yake yi wa manema labarai bayani bayan kammala taron nasu a ranar Talata, Sakataren BoT na Jam’iyyar, Babayo Muhammed Abdulahi, ya zargi Kwankwaso da yin ta’ammali da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar da kuma ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar Labour, Mr. Peter Obi ba tare da izinin kwamitin ba.
Daga nan, Abdullahi ya sanar cewa kwamitin ya sauke Kwankwaso a matsayin shugaban NNPP na ƙasa.
Ya ƙara da cewa an dakatar da mu’assasin jam’iyyar ne saboda saɓa dokokin jam’iyyar.