NNPP ta kori ɗan takarar mataimakin gwamna na jam’iyyar da wasu ƙusoshinta a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Jam’iyyar NNPP a Jihar Katsina ta kori wasu jiga-jigan jam’iyyar ciki har da mataimakin ɗan takarar gwamnan jihar, Muttaqa Rabe Darma da shugaban jam’iyyar, Alhaji Sani Liti da sakatarenta Alhaji Mustapha Bashir da kuma shugaban matasa da shugabannin jam’iyyar na shiyyoyin Katsina, Daura da kuma Funtua.

Kakakin jam’iyyar, Alhaji Nasiru Usman Kankia ne ya bayyana wa manema labarai hakan lokacin da yake ƙarin bayani dangane da lamarin a Katsina.

A cewar kakakin, an kori mutanen ne bisa aikata laifin yi wa jam’iyya zagon ƙasa.

Ya ƙara da cewa shugabannin jam’iyyar sun kira wani taron da baya kan ƙa’ida inda suka amince da goya wa wani ɗan takarar gwamna na wata jam’iyya baya.

Ya kuma ce shugaban jam’iyyar ya kira wani taro don tattauna yadda za a biya wakilan jam’iyyar da suka yi aikin zaɓen Shugaban Ƙasa.

“Sun kira taron shugabannin Jam’iyyar na ƙananan hukumomi ne inda suka bayyana masu cewar maƙasudin taron shi ne don a tattauna yadda za a biya waɗanda suka yi aikin zaɓe”. Inji shi.

Ya ƙara da cewa daga nan sai kawai aka ga ɗan takarar gwamnan jihar a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Dikko Umar Raɗɗa ya shigo taron.

“A taron wanda aka shirya ba bisa ƙa’ida ba, sai aka hango ɗan takarar jam’iyyar APC ya shigo wurin inda shugaban jam’iyyar na NNPP da kuma mataimakin xan takarar gwamnan jihar da sauran shugabannin Jam’iyyar suka gabatar wa Raɗɗa mahalarta taron a matsayin waɗanda suka sauya sheƙa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.” Inji shi.

Ya kuma ce a nan ne suka bayyana cewar maƙasudin shirya taron don goya wa ɗantakarar jam’iyyar APC baya ne

Nan da nan mahalartar taron suka nuna rashin amincewar su don ba abinda ya kawo su ba kenan daga bisani wurin taron ya hargitse da hayaniya kamar yadda kakakin jam’iyyar ya bayyana

Sai dai fan takarar gwamna a jam’iyyar APC ya bayyana cewar tattauna yadda za a yi ƙawance tsakanin jam’iyyun biyu ne ya kawo shi wurin taron ba wai zawarcin ‘yan jam’iyyar ta NNPP ba.

A yayin da kakakin jam’iyyar na NNPP ya ce tun farko sun gargaɗi ‘yan jam’iyyar da kuma shugabanninta dangane da yin kowane irin ƙawance da kowace jam’iyya.