Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA), ta bai wa jami’anta da ke ƙananan hukumomi 774 da ake da su a Nijeriya umarni a kan su haddace sabon taken ƙasa a tsakanin sa’o’i 72, wato ya zuwa 3 ga watan Yuni.
Ta ce jami’anta da ke yankunan karkara su ne su tabbatar da ɗabbaƙa sabon taken ƙasar daga tushen al’umma.
Kazalika, hukumar ta ce, “muna aiki tare da Ƙungiyar Malamai ta Ƙasa (NUT) wajen tabbatar da makarantun faɗin ƙasar nan sun fara amfani da sabon taken na ƙasa.”
Cikin sanarwar da hukumar ta fitar, an jiwo Mataimakin Daraktan Yaɗa Labarai, Paul Odenyi, ya naƙalto Shugaban Hukumar NOA na Ƙasa, Lanre Issa-Onilu, na cewa, umarnin ɓangare ne na ƙoƙarin da hukumar ke yi wajen gabatar da sabon taken ga ‘yan ƙasa.
Issa-Onilu ya ce, maido da tsohon taken na ƙasa na daga cikin manufofin da gwamnati ke da su na cusa kishin ƙasa a zukatan ‘yan Nijeriya.
A ranar Laraba Shugaban Ƙasa Tinubu ya rattaɓa hannu kan dokar da ta maido da tsohon taken ƙasar da aka yi amfani da shi shekarun baya.