Noma da kiwo ne babbar hanyar cigaba, inji Hon. Kibiya a taron ƙungiyar OWSI

Daga MUHAMMADU MUJITABA

Tsohon kwamishinan al’amuran gona a Kano a 1999 zuwa 2003, Honarabul Yusuf Ado Kibiya, ya bayyana cewa, a kullum addu’a muke yi man fetur ya ƙari domin shi ne ya kawo mana koma baya a harkar noma da kiwo a Nijiriya wanda kafin man fetur, Arewa da ma Nijiriya na alfihiri da kayan gona a matsayin arzikinmu mai ɗorewa, wanda yake daga gano man fetur abun ya koma baya kuma barin noma a kama wani abu matsala ce wanda kuma wannan matsala ce babba a wajen cigaban ƙasa.

Hon. Yusuf Ado Kibiya ya yi wannnan bayanin ne da yake jawabi wajen taron da ƙungiyar OWSI ta shirya a gidan mubayya a ranar Lahadi da ta gabata.

Har ila yau, ya ce, mu anan Arewa inda aka bunƙasa noma da kiwo aka ce ana samun wadatarciyar madara, to don ba man fetur ba wata matsala domin yanzu haka duk da ta shin gwaron zabi na man fetur a ƙasar nan amma dai Litar madara ɗaya tafi man fetur daraja kuma samar da madara zai ba jama’ar mu aikin yi kuma a daina mana gorin man fetur, domin shi ma da kuɗin noman gyaɗa aka gano shi aka haƙo shi, wanda Nijeriya gaba ɗaya ke cin moriyarsa a yau.