Noma: Shugaba Buhari ya bayyana dalilin tashin farashin abinci a Najeriya

Daga AMINA YUSUF ALI

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana dalilin da ya sa a kullum ake samun hauhawar farashin abinci a ƙasar Najeriya duk da yadda jama’a suka tsunduma ka’in da na’in wajen noma kayan abinci a ƙasar.

Wannan jawabi yana ƙunshe ne a cikin jawabin da Shugaban ya gabatar a ranar murnar zagayowar samun ‘yancin Najeriya Karo na 61 wanda ya gudanar ranar 1 ga watan Oktoba l, 2021 wato Juma’ar da ta gabata, a Abuja. Inda shugaban ya bayyana cewa, ba wasu ne suke jawo wannan tsadar rayuwar ba illa dillalai. Domin a cewar sa, su ne suke ɓoye abinci da gangan domin ya yi wahala a sayar da shi da tsada, su kuma su ci ƙazamar riba. 

Shugaban ya nuna takaicinsa da wannan mummunan halin nasu na rashin kishin ƙasa. Da suke ɓoye abinci suna sa ‘yan ƙasa a cikin wahala. Amma a cewar sa, Gwamnatin Tarayya ta shirya tsaf domin ɗaukar matakin sanya zare da duk masu waccan ɗabi’a ta ɓoye abinci da gan-gan. Sannan kuma ta tabbatar da cewa ‘yan Najeriya sun wadata da isasshen abinci.

Buhari ya ƙara da cewa, Gwamanatin Tarayya tana sane da yadda farashin abinci yake ƙara hauhawa kuma za su ɗauki matakin daƙile shi.

A cewarsa dole a bunƙasa sashen noma domin shi ne tushen arzikin kowacce ƙasa.