Noman rani: Gwamna Sule ya ƙaddamar da shirin saida takin zamani

Daga BASHIR ISAH

A matsayin wani mataki na bunƙasa noman rani a 2022 a jaihar Nasarawa, Gwamnan Jihar, Engr. Abdullahi A. Sule, ya ƙaddamar da shirin sayar da takin zamani don tallafa wa manoman rani a jihar.

Ƙaddamarwar ta shafi har da sauran kayayyakin aikin gona, inda gwamnan ya bayyana farashin takin kan N7000 ga kowane buhu.

Sa’ilin da yake jawabi, A.A Sule ya yi kira ga manoman da za su ci gajiyar shirin da su yi amfani da wannan dama wajen ci gaba da wadata jihar da kewaye da abinci.

Taron ƙaddamarwar ya gudana ne a harabar hedikwatar cibiyar kula da harkokin noma ta NADP da ke hanyar Agyaragun Tofa, Lafia babban birnin jihar.

Yayin taron, an shaida raba wa manoman da suka cancanta kayayyakin, yayin da su ma manoman suka bada tabbacin yin amfani da kayayyakin yadda ya kamata. Taron ya samu mahalarta daga sassa daban-daban kuma ya kammala cikin nasara.