Noman rani: Gwamnatin Katsina za ta faɗaɗa madatsan ruwa na Ɗanja

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina za ta faɗaɗa madatsan ruwa na ƙaramar hukumar Ɗanja domin faɗadɗa noman rani a yankin.

Gwamna Dikko Umar Raɗɗa ya faɗi hakan a garin Ɗanja, lokacin da ya ke ƙaddamar da tallafin Naira miliyan 20 da ɗan Majalisar Dokoki na jihar mai wakiltar Ɗanja, Hon. shamsuddeen Abubakar ya raba.

Ya ce gwamnatinsa ta na sane da yanayi mai kyau na ƙasar noma da ke yankin.

“wannan shiri kashi ne na biyu zai haɓaka noman rani a yankin, kuma zai bunƙasa tattalin arziƙin ba ma manoma ba kaɗai, har da sauran al’ummar yankin”, inji gwamnan.

Dikko Raɗɗa ya yaba wa dan majalisar bisa ƙoƙarin da ya ke yi na bunƙasa tattalin arziƙi a mazaɓarsa.

A jawabin ɗan majalisar, ya ce cikin kayan da zai raba na adadin kuɗin sun haɗa da; magungunan feshi guda 150 da kekunan ɗinki da kurayen ɗaukar kaya ( Wheel barrows) da sauran su.

Ya ce, mata da matasa da suke noma da kiwo da kuma ɗinki za su amfana da tallafin.

Ɗan majalisar ya yi alƙawari ga waɗanda ba su samu ba cewa zai tabbatar a kashi na biyu na rabon kayan sun amfana.

Shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Rabo Tambaya Ɗanja ya yaba wa gwamnatin Dikko Raɗɗa kan yadda take ƙoƙari wajen shawo kan ta’addanci a jihar da alkawarin gina ofishin jami’an tsaron al’umma CWC a karamar da ta yi.