NPCF ta ayya Muslihu Ali don naɗa shi Ministan Matasa

Ƙungiyar kansiloli ta ƙasa, wato National Progressive Councilor’s Forum (NPCF), ta buƙaci a naɗa shugabanta Hon Muslihu Yusuf Ali a muƙamin Minista a Gwamnatin Tarayya.

A cewar ƙungiyar ta ce ta ayyana Muslihu don naɗa shi minista ne biyo bayan sanar da sake Ministan Matasa da Shugaba Bola Tinubu ya yi ba tare da ya bayyana da ko wane ne ba.

NPCF ta bayyna haka ne cikin sanarwar manema labarai da ta fitar mai ɗauke da kwanan wata 26 ga Agusta, 2023 da kuma sa hannun Sakataren ƙungiyar na ƙasa, Hon Abayomi kazeem.

A cewarta, “La’akari da sanarwar da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar mai ɗauke da kwanan wata 20 ga Agusta, 2023 wadda ta ce Shugaban Ƙasa Asiwaju Ahmed Bola Tinubu ya sake ministan matasa amma bai bayyana wane ne sabon ministan ba.

“A madadin kansilolin Jam’iyyar APC a faɗin ƙasa, Kwamitin Gudanawa na NPCF ya ayyana Hon Muslihu Yusuf Ali wanda ke da cancanta da ƙwarewa a sha’anin shugabanci da siyasa wanda kuma ya riƙe muƙamai daban-daban a matakin ƙaramar hukuma, jiha da kuma ƙasa don naɗa shi muƙamin.

Muslihu kansila ne daga Jihar Kano mai wakiltar jama’ar Gundumar Guringawa cikin ƙaramar hukumar Kumbotso a jihar.

Kansilolin sun ce muddin Tinubu ya naɗa nasu wannan muƙamin, suna tabbatar masa sake samun ƙiri’un matasa miliyan 10 a 2027 idan Allah Ya kai mu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *