NRC ta gyara layin dogon Abuja-Kaduna, ta gindaya sabbin sharaɗɗan sayen tikiti

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ƙasa ta Nijeriya (NRC), ta ce, ta gyara ɓarnar da aka yi wa na’urorin layin dogon Abuja zuwa Kaduna, da kuma sanya sabbin sharuɗɗa na sayen tikiti.

Har ila yau, ta tabbatar da cewa, fasinjojin da ke son shiga za su gabatar da Lambar Shaida ta Ɗan Ƙasa (NIN), a matsayin wani sharaɗi na sayen tikitin jirgin ƙasa.

Rahotanni sun nuna cewa, an yi matuƙar lalata layin dogon a kwanan nan sakamakon harin da maharan suka kai.

Manajan Daraktan NRC, Injiniya Fidet Okhiria ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Kaduna.

Wani ɓangare na sanarwar ya ce, “an samu nasarar haɗe ƙarshen layin dogon titin (wanda fashewar ta lalata, kuma yanzu an dawo da hanyar da ke tsakanin Abuja da Kaduna.

Shugaban na NRC, ya bayyana cewa, hukumar jirgin ƙasa ta Abuja zuwa Kaduna (AKTS) za ta dawo nan ba da daɗewa ba tare da samar da ƙarin matakan tsaro, kuma wannan buƙata ta NRC za ta taimaka wajen inganta bayanan fasinja da kare lafiyar fasinjoji a cikin jirgin.