Daga UMAR GARBA a Katsina
Hukumar tsaron wato NSCDC ta karrama wasu daga cikin jami’anta da suka samu ƙarin girma.
Bikin karramawar ya gudana a ranar Talata, 29, ga watan Oktoba,2024.
Da yake jawabi kwamandan hukumar a Katsina, Jamilu Indabawa ya buƙaci waɗanda aka yi wa ƙarin girman akan su kasance masu ɗa’a, aiki tuƙuru da kuma gujewa karɓar rashawa a yayin aikin.
“Dole ku kasance masu ɗa’a, da yin aiki tuƙuru don ɗaga martabar wannan hukuma don karewa, tare da tsare lafiyar al’umar Jihar Katsina da ma Nijeriya.” Inji kwamandan.
A cewar shi wannan ƙarin girma da aka yi wa jami’an hukumar ta NSCDC ya tabbatar da ƙudurin babban kwamandan hukumar, Ahmed Abubakar Audi na inganta aikin jami’an.
A cewar Indabawa, tun da Abubakar Audi ya kama aiki a matsayin babban kwamandan hukumar ya duƙufa wajen inganta jin daɗin jami’an gami da sauya fasalin hukumar don ingantuwar ayyuka.
A saƙonsa shugaban kwalejin wanzar da zaman lafiya da kare afkuwar Ibtila’i, ACG Babangida Abdullahi ya taya waɗanda aka yi wa ƙarin girman murna ya kuma buƙace su akan su ɗauki wannan karramawa a matsayin abunda zai ƙara masu ƙaimi don ninka ƙwazonsu wajen kare lafiya da dukiyar al’umar Jihar Katsina dama ƙasa baki ɗaya.
Kazalika kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Aliyu Abubakar Musa ya bayyana muhimmancin hukumar ta NSCDC a matsayin ɗaya daga cikin hukumonin dake samar da tsaro a jihar.
Daga nan sai ya buƙaci jami’an na NSCDC a kan su kasance cikin shirin ko ta kwana don kare ƙasarsu.
Daga cikin waɗanda aka ƙara wa girman akwai mataimakan kwamandan hukumar (DCC) guda shida, mataimakan kwamandan II (ACC) guda uku da dai sauran muƙamai.