NUJ ta dakatar da yaɗa harkokin ‘yan sanda kan cin zarafin ɗanta a Bauchi

Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ) reshen Jihar Bauchi, ta bai wa mambobinta umarnin nan take da su daina yaɗa harkokin ‘yan sandan a faɗin jihar.

Cikin wata sanarwar manema labarai da ƙungiyar ta fitar a Juma’ar da ta gabata, shugaban ƙungiyar a jihar, Comrade Umar Sa’idu tare da sakatarensa, Isah Garba Gadau, sun bayyana rashin jin daɗinsu dangane da yadda ‘yan sandan jihar suka ci mutunci wani ɗan jarida a jihar wanda ma’aikaci ne a tashar talabijin ɗin AIT.

‘Yan sandan rundunar RRS sun lakaɗa wa Damina Yusuf duka da ji masa rauni ne a lokacin da yake ƙoƙarin ɗaukar bayanai kan zanga-zangar da ɗaliban Kwalejin Harkokin Gona ta Bauchi da ke Yelwa suka gudanar ran Alhamis da ta gabata.

Bayan aukuwar lamarin, daga bisani an ɗauki ɗan jaridar zuwa Asibitin Koyarwa ta Tafawa Ɓalewa (ATBUTH) da ke Bauchi don yi masa magani.

Bisa wannan dalili ne NUJ reshen jihar Bauchi ta nuna damuwarta tare da yin tir kan yadda ‘yan sandan suka yi wa ɗanta dukan kawo wuƙa, wanda hakan ya sanya ita kuma ta ɗauki matakin umartar mambobinta a jihar da su dakatar da yaɗa harkokin ‘yan sanda a jihar baki ɗaya.

Bayanan NUJ sun nuna yayin badaƙalar, ‘yan sandan sun ƙwace wa ɗan jaridar kayayyakin aikinsa da suka haɗa da kamara da kwamfuta da wayoyi da kuɗi da dai sauransu.

A hannu guda, NUJ ta yaba wa
hukumar Kwalejin Harkokin Gona ta Bauchi bisa kulawar da ta nuna inda ta ɗauki Yusuf zuwa asibiti don duba lafiyarsa.

A ƙarshe, NUJ ta buƙaci Gwamnantin Jihar Bauchi da ta kafa wani kwamiti na musamman wanda zai riƙa bincike kan yadda ake cin zarafin ‘yan jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *