NUJ ta yi gargaɗin a sako mata ɗanta da aka sace

Daga AISHA ASAS

Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ) reshen Birnin Tarayya, Abuja, ta yi kira da a gaggauta sako mata ɗanta Okechukwu Nnodim ma’aikaci a Jaridar Punch.

Bayanan da suka fito daga ƙungiyar sun yi zargin cewa har gida wasu ‘yan bindiga suka bi Nnodim suka yi gaba da shi, bayan da suka yi harbe-harbe a iska da bindigoginsu.

Takardar da ƙungiyar ta fitar wadda shugabanta Comrade Emmanuel Ogbeche da sakatarenta Ochiaka Ugwu suka sanya wa hannu, ta nuna yadda ƙungiyar ta yi tir da wannan ɗanyen aiki, tare da neman a sako Nnodim ba tare da wani sharaɗi ba.

Ƙungiyar ta ce babu wani dalili da zai sa a sace ɗan jarida hasali ma ‘yancin walwala na daga cikin sharuɗɗan aikin jarida da kan bai wa ‘yan jarida damar gudanar da harkokinsu yadda ya kamata ba tare da wata takura ba.

Don haka NUJ ta buƙaci a ɗauki matakan da suka dace wajen gano waɗanda ke da hannu a batun sace Nnodim domin bai wa ‘yan jarida zarafin yin aikinsu kamar yadda doka ta tanada.