NUJ ta yi kira ga NBC da ta janye tarar milyan 5 da ta ɗora wa tashar Channels

Daga AISHA ASAS

Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ) ta yi kira ga Hukumar Kula da Kafafen Yaɗa Labarai ta Ƙasa (NBC) da ta tsananta lura game da yadda take ɗaukar mataki a kan kafafen yaɗa labarai a cikin ƙasa.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Chris Isiguzo, ya ce sun yi mutuƙar damuwa da barazanar da hukumar NBC ta yi na dakatar da lasisin tashar talabijin ta Channels saboda tattaunawar da ta yi da mai magana da yawun tsegerun IPOB a wani shirinta da tashar ta gabatar kwanan nan.

NUJ ta ce tana buƙatar NBC ta gaggauta janye tarar milyan N5 da ta ɗora wa tashar sakamakon laifin da ta ce ta aikata.

Cikin sanarwar da NUJ ta fitar a wannan Talatar mai ɗauke da sa hannun shugabanta na ƙasa Chris Isiguzo, shugabanta ya ce duk da dai ba su son wani abu da zai haɗa su da hukumar NBC, amma suna gargaɗin cewa irin wannan barazana ka iya haifar da tashin-tashina a cikin jama’ar da da ma a dabaibaye take da matsaloli iri daban-daban.

Ya ci gaba da cewa, a irin wannan mawuyacin hali da ƙasa ke ciki, abin da ya kamace NBC shi ne ta samar da ƙarin damarmakin da za su bai wa ‘yan Nijeriya zarafin kafa kafofin yaɗa labarai masu zaman kansu da ‘yanci da za su yi gogayya da takwarorinsu.

Ya ce duba da yadda NBC ta ƙaƙaba wa kafofin yaɗa labarai takunkumai a baya-bayan nan, hakan ya nuna dokar NBC ɗin ba ta yi daidai da batun ‘yancin faɗar albarkacin baki da kuma ‘yancin ‘yan jarida ba wanda akwai buƙatar a duba don a yi gyara.

A hannu guda, NUJ ta yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su yi ƙoƙarin ganin cewa suna gudanar da ayyukansu daidai da doka kuma kada su bari ‘yan siyasa su yi wasa da hankulansu wajen lalata dimukuraɗiyyar ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *