NURTW ta fara shirin rage cunkuso a Maraba

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Ƙungiyar direbobin motocin sufuri ta ƙasa da aka fi sani da (NURTW) ta ce, ta ɗauki ƙwararan matakai don rage cunkosun ababen hawa da ake yawan fuskanta a garin Maraba da ke yankin ƙaramar hukumar Karu a jihar Nasarawa.

Sakataren shirye-shirye na ƙungiyar a jihar Nasarawa, Alhaji Abdullahi Gandu ne ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci mambobin ƙungiyar inda suka ƙaddamar da wani shiri na musamman don shawo kan lamarin. Shirin wadda suka yi wa lakabin ‘OPERATION PARK WELL’ a turance, an gudanar da shi ne a ƙarƙashin wani babban gada da ke tsakiyar garin ta Maraba ranar Lahadi da ta gabata wato 21 ga watan Nuwambar shekarar, 2021, da ake ciki.

Alhaji Abdullahi Gandu bayan ya yaba wa gwamnatin jihar dangane da alƙawari da ta yi musu kwanan nan na gina kimanin tashoshin ababen hawa 24 a garin Maraba nan bada daɗewa ba don magance lamarin inda ya ce, ba shakka idan aka yi haka zai je nesa ba kusa ba wajen rage matsalar cunkusun a garin da kewayen ta baki ɗaya.

Itama a nata ɓangaren da ta ke jawabi wata babbar jami’ar hukumar kare haɗurra a yankin na Maraba, misis Ngwankwe Ake ta bayyana takaicinta ne dangane da rashin ji da halin ko-in-kula da al’ummar Maraban ke nuna musamman na kin bin ta gadadi ayayin da suke ƙetare babban titin garin zuwa ɓangare na biyu. Maimakon haka a cewarta sau da yawa za a ga suna bin ta ƙarƙarshin gadan ne da hakan acewarta kan mayar da hannun agogo baya a ƙoƙari da hukumar ke yi na rage cunkusun.

Daganan sai ta yi amfani da damar inda ta buƙaci gwamnatin tarayya ta hanzarta kammala aikin faɗaɗa babban hanyan Abuja zuwa Makurdi da ta ke yi a yanzu don shawokan matsalar.

Wakilinmu dai ya lura cewa, garin Maraba gari ne da ke yawan samun cunkusun ababen hawa da hakan kan jawo wa al’ummar yankin da sauran matafiye babban matsala a yayin da suke gudanar da ayukan su na yau da kullum.