NUSAID ta tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi 750 da kayan abincin azumi a Kano

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wata ƙungiya mai zaman kanta a Jihar Kano mai suna NUSAID tare da haɗin gwiwar Zauren Hadin Kan Malaman Kano a ranar Lahadi ta raba kayan abinci da kuɗi a matsayin tallafin azumi ga mutum 750 a Kano.

Mutanen, waɗanda suka haɗa da mata da marayu da sauran masu ƙaramin ƙarfi dai sun rabauta da kayan ne a wani vangare na tallafin da ƙungiyar ta saba bayarwa kowacce shekara a watan azumi.

A cewar mai kula da tsare-tsare na ƙungiyar, Dokta Sa’idu Ahmad Dukawa, sun raba kayan tallafin ne domin su rage raɗaɗin rayuwa ga mabuƙata musamman a watan azumi.

Ya ce, “Wannan ta jima tana bayar da tallafi a kowanne watan azumi da kuma duk lokacin da buƙatar hakan ta taso tun shekara ta 2016, kamar lokacin da aka fuskanci iftila’in ambaliya a Jihohin Kano da Katsina da Jigawa a bara.

“Mutum 750 ne suka rabauta da wannan tallafin a yau, kuma abin da ke ciki kayan abinci ne sai ’yan kuɗin mota. A cikin kowanne ƙunshi akwai shinkafa da taliya da man gyaɗa da dabino, sukari da kuma gishiri.

“Babbar manufarmu ta yin wannan aikin alherin ita ce ta rage wa masu azumi raɗaɗin halin da suke ciki, musamman a wannan watan na azumi,” in ji Dakta Dukawa.

Wasu daga cikin waɗanda suka amfana da tallafin bayyana farin cikinsu musamman kasancewarsa a watan azumi, inda suka buƙaci sauran ƙungiyoyi da sauran masu hannu da shuni da su yi koyi da ƙungiyar.