Obasanjo ya buƙaci a soke sakamakon zaɓe a wuraren da na’uran BVAS ta samu matsala

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ya yi kira ga Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Yakubu Mahmood, da ya bayyana soke sakamakon zaɓe a rumfunan da hukumar zaɓen ta samu matsalar aiki da na’urar BVAS a zaɓen ranar Asabar da ta gabata. Zaɓen Shugaban Ƙasa da na ‘yan majalisun tarayya.

Obasanjo a wata wasiƙa da ya fitar a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun a ranar Litinin, ya yi kira ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da ya kauce wa abin da ya kira hatsarin da ke kunno kai na ba da umarnin soke sakamakon zaɓe a duk zaɓukan da ba a yi su na gaskiya da gaskiya ba.

“Bari in yi kira ga Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), idan har yana son zama tsaftatacce, ya ceci Nijeriya daga cikin haɗari da bala’in da ke neman faruwa. Idan Shugaban Ƙasa zai iya ɗage zaɓen kwanaki huɗu, zai iya yin duk abin da ya dace don gyara kurakuran da aka yi a cikin kwanaki biyun da suka gabata, idan ba a yi amfani da BVAS, babu sakamakon da za a yarda da shi; kuma babu loda shi ta hanyar ‘Server’ ɗin INEC, babu sakamakon da za a yarda.

“Duk da cewa an yi amfani da BVAS da Servers ko kuma an mayar da su ba sa aiki, dole ne a bayyana irin wannan sakamakon a matsayin mara amfani kuma ba za a yarda da shi ba, don bayyana zaɓe. Shugaban INEC, na yi tunanin cewa za ka yi amfani da wannan dama mai kyau wajen gyara mutuncinka da halayenka na baya.

“Maigirma Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, tashin hankali yana ƙara ta’azzara, don Allah a soke duk zavukan da ba na gaskiya da gaskiya ba, a dawo a sake su a wuraren da aka tafka maguɗi a ranar Asabar mai zuwa, 4 ga Maris, 2023.

“A canza na’urar BVAS da Server. Domin sanin ko wace rumfunan zaɓe ko rumfunan zaɓen da aka yi amfani da su, bari kwamitin ma’aikatan INEC da wakilan manyan jam’iyyun siyasa huɗu tare da shugaban ƙungiyar lauyoyin Nijeriya su duba abin da ya kamata a yi domin gudanar da zaɓe a ranar Asabar mai zuwa. Ya mai girma Shugaban Ƙasa, da fatan shirinka na yin zaven gaskiya da gaskiya ya tabbata don barin gadon mulkinka cikin nasara.”

Obasanjo ya cigaba da cewa: “Malam Shugaban Ƙasa, kada ka bari wani ya ce maka ba komai ko matsalar INEC ce. Babu wani dalili da ya kamata a gan ku a matsayin wani ɓangare na haɗin gwiwa ko sasantawa. Lokacin da aka kashe, zai zama matsalarka a matsayinka na Babban Jami’in Gudanarwa na Ƙasa.”

Ya kuma yi nuni da cewa Shugaban INEC zai iya kawo wa ƙasar cikas wajen haddasa fitina.