Ododo ya zama ɗan takarar gwamna na APC a Kogi

Tsohon Odita Janar na Gwamnatin Jihar Kogi, Usman Ododo, ya lashe zaɓen fidda gwani na takarar Gwamna da Jam’iyyar APC ta shirya a jihar.

Zaɓen fidda gwanin ya gudana ne a gundumomi 239 a tsakanin ƙananan hukumomi 21 da jihar ke da su.

Ododo ya lashe zaɓen ne da ƙuri’u 78,704 inda ya doke sauran abokan hamayyarsa su shida.

Ododo na hannun daman Gwamna Yahaya Bello ne wanda ya tsayar da shi takara ‘yan kwanaki kafin zaɓen.

Sakataren Kwamitin Zaɓen Fidda Gwani na takarar gwamna na Jam’iyyar APC, Patrick Obahiagbon, shi ne ya bayyana sakamakon zaɓen, inda ya ce baki ɗaya masu zaɓe 93,729 aka yi wa rijista, yayin da aka tantance mutum 83,419 a lokacin zaɓen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *