Ofishin jakadancin dake Amurka ya ƙaryata kalaman Dda Amurka ta yi kan rikicin Rasha da Ukraine

Daga CMG HAUSA

Mai magana da yawun ofishin jakadancin ƙasar Sin dake ƙasar Amurka, ya mayar da martani kan tambayoyin da manema labaru suka yi jiya Talata, inda ya musanta bayanin da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta yi a ranar Litinin 2 ga wata cewa, wai jami’ai da kafofin watsa labaru na ƙasar Sin suna yada farfaganda da bayanan ƙarya na Rasha, a yayin rikici tsakanin ƙasashen Rasha da Ukraine.

Kakakin ya ce, matsayin ƙasar Sin kan batun Ukraine yana bisa gaskiya da adalci, kuma babu wani abin zargi a ciki. Idan ana batun yada bayanan ƙarya ne, ya kamata Amurka ta yi tunani sosai a kai. Amurka ta ƙaddamar da yaki a kasashen Iraki, da Afganistan da Siriya tsawon shekaru, inda aka kashe fararen hula 335,000. Wannan ba labarin ƙarya ba ne. Galibin ƙasashe a duniya suna bayar da shawarwari kan yadda za a warware rikicin da ke tsakanin Rasha da Ukraine ta hanyar tattaunawa da shawarwari, kuma ba sa son ganin lamarin ya ƙara ta’azzara, ko ma ya shiga wani hali, wannan ma ba labarin ƙarya ba ne.

Jami’in ya ce, a watan Nuwamban shekarar 2021, ƙasar Amurka ta mika takardar bayanin aiki ga taron ƙasashen da suka kulla yarjejeniyar taƙaita yaɗuwar makaman kare dangi, tare da sanin cewa, ƙasar Amurka na da dakunan gwaje-gwajen ƙwayoyin halittu guda 26 da sauran cibiyoyin haɗin gwiwa a Ukraine. Wannan ba bayanin ƙarya ba ne.

Don haka, ya kamata Amurka ta yi marhabin da al’ummomin duniya don gudanar da bincike cikin haɗin gwiwa ƙarƙashin tsarin MDD da yarjejeniyar takaita yaɗuwar makamai masu guba.

Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa