Ofishin jakadancin Falasɗinu a Nijeriya ya yi Allah-wadai da kisan da Isara’ila ke yi wa Falasɗinawa

*Ya nuna alhini kan sace ɗaliba a arewacin Nijeriya

Daga BASHIR ISAH

Ofishin Jakadancin Falasɗinu a Nijeriya ƙarƙashin Abdullah M. Abu Shawesh, ya tir da irin kisan kiyashin da Isra’ila ke yi wa Falasɗinawa.

Cikin sanarwar da ya fitar a ranar Juma’a, ofishin ya fara bayani ne da nuna alhininsa kan ɗaliban da aka sace da sauransu a yankin Arewa.

Abdullah M. Abu Shawesh ya ce, “Jin irin wannan labari yana motsa ni sosai kuma yana ƙara baƙin cikina

“A cewar dokar Yahudawa, dole ne a kashe dukkan mazauna Gaza.”

“Hukumomin Isra’ila sun amince da wannan nau’in tunzura jama’a, kuma jama’a da dama sun amince da shi. Wannan dai ba shi ne karon farko da malaman addinin yahudawan ke fitowa fili domin tunzura al’ummar Palastinu da ba su ji ba ba su gani ba.

“Abin lura ne cewa Isra’ila na daure duk wani Bafalasdine saboda kawai ta tausayawa wadanda yakin ya rutsa da su a shafukan sada zumunta bisa hujjar tunzura su.

“Al’ummar Yahudawan Isra’ila suna ƙasƙantar da kai ga ƙarin tsattsauran ra’ayi yayin da duniya baki ɗaya ke adawa da mamayar Rafah.

“Kashi 75% na Yahudawan Isra’ila suna goyon bayan wannan laifin yaƙi “Wani sabon bincike ya gano cewa kusan kashi uku cikin huɗu na Yahudawa Isra’ilawa suna goyon bayan faɗaɗa ayyukan IDF a birnin Rafah da ke kudancin Gaza, inda fiye da rabin mutane miliyan 2.3 na Zirin ke mafaka a yankin a cikin yaƙin da ake yi.”

Ya ƙara da cewa, “Ya zuwa yau, 14 ga Maris, an samu shahidai 31,272, yayin da 73,024 suka samu raunuka, sannan kashi 72% da yaƙin ya ritsa da su yara da mata ne.

“Kawo yanzu, ba a gano fiye da mutum 8,000 da ke ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine ba, kuma a lokuta da dama Isra’ila na hana jami’an ceto isa gare su ko kuma kwashe gawarwaki.

“Yaran da aka bayar da rahoton kashe su a cikin sama da watanni huɗu a Gaza ya zarce adadin yaran da aka kashe a yakin shekaru 4 a duniya baki ɗaya. Wannan yaƙi, yaƙi ne a kan yara.”

Haka nan, ya ce, “Philippe Lazzarini, Babban Kwamishinan UNRWA, ya ce adadin ƙananan yaran da suka mutu a Gaza sakamakon rashin abinci mai gina jiki da fari ya kai 23. kuma wasu sun mutu a gida ba a yi musu rajista ba.

“Ya zuwa ranar 6 ga Maris, adadin ma’aikatan UNRWA da aka kashe tun farkon tashin-tashinar ya kai 162.

“Daga tsakanin 7 ga Oktoba 2023 zuwa 6, ga Maris 2024, an kashe Falasɗinawa 415, ciki har da aƙalla yara 106 a Yammacin Kogin Jordan.

“Ya zuwa ranar 12 ga Maris, adadin mutanen da ake tsare da su a Yammacin Gaɓar Kogin Jordan ya kai 7,555, ciki har da mata 240, da yara 500, da ‘yan jarida 22 da aka yanke wa hukuncin ɗaurin rai-da-rai, da kuma wasu 37 da har yanzu ake tsare da su.

“A cikin kwanaki 160 da suka gabata, an ba da umarni sama da 4,122 na tsare a hannun gwamnati. Fursunoni 12 ne suka mutu a sansanonin da ake tsare da su a Isra’ila da kuma gidajen yari.

“Dangane da fursunonin Gaza dai, babu wani bayani da aka samu saboda kin bayar da wani bayani da Isra’ila ta yi da kuma yadda suke bi ta tilas,” in ji shi.