Ofishin Jakadancin Sin a Sudan ta Kudu ya gina rijiyar sada zumunta a wani gidan marayu

Daga CMG HAUSA

A baya-bayan nan ne aka ƙaddamar da wata rijiya da aka yi wa laƙabi da “Rijiyar ƙawancen Sin da Sudan ta kudu”, a wani gidan kula da marayu dake birnin Juba, fadar mulkin Sudan ta Kudu.

Ofishin jakadancin Sin dake ƙasar ne ya aiwatar da ginin rijiyar, bayan samun labarin cewa, yaran dake zaune a gidan na rayuwa cikin yanayi na rashin ruwa.

A cewar shugaban makarantar dake gidan marayun Jacob Mijok, ruwan da yaran ke amfani da shi a baya, ba shi da cikakkiyar tsafta, ga kuma zartsi. To sai dai kuma da jin hakan, ofishin jakadancin Sin ya yi hoɓɓasa wajen gina sabuwar rijiya mai nagarta ga marayun.

Game da hakan, jakadan Sin a Sudan ta kudu Hua Ning ya ce, burin Sinawa ne, da al’ummar Sudan ta kudu, da ma ɗaukacin al’ummun Afirka, su ga yara marayu sun girma cikin kyakkyawan yanayi.

Mai fassarawa: Saminu daga CMG Hausa