Ogun: Haɗari ya ci ran mutum biyu, an ƙona motar da ta yi kisan

Daga WAKILINMU

Wasu fusatattun mutane sun banka wa wata babbar motar ɗaukar kaya wuta biyo bayan haɗarin da ya auku wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyu a jihar Ogun.

Haɗarin ya auku ne a hanyar Ibeshe da ke yankin ƙaramar hukumar Yewa ta Arewa a Asabar da ta gabata.

Bayanan da Manhaja ta kalato sun nuna motar ta saki hannunta ne ta koma ɗaya hannun inda ta sami wasu mutum biyu a kan babur ta murƙushe su har lahira.

Mai magana da yawun rundunar kula da bin dokoki na jihar, Babatunde Akinbiyi, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Abeokuta, babban birnin jihar.

Ya ce ganin munin abin da ya faru ya sa wasu fusatattu suka sauke wa motar fushinsu suka ƙona ta, yayin da direban motar ya ranta a na kare don tsira da ransa.

Ya ci gaba da cewa sai da ‘yan sanda da jami’an tsaron farar hula suka agaza kafin aka samu aka kwantar da ƙurar da ta tashi a wajen da haɗarin ya faru.

Akinbiyi ya ƙara da cewa an kai gawar ɗaya daga cikin waɗanda haɗarin ya rutsa da su ajiya a Babbar Asibitin Ilaro, sannan ɗayar kuma tuni ‘yan’uwa sun karɓa sun binne ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *