Ogun: Matar da ta babbaka mijinta da tafasasshen ruwa ta faɗa a komar ‘yansanda

Daga WAKILINMU

‘Yansandan Jihar Ogun sun cafke wata mata ‘yar shekara 43 mai suna Bisola Awodele bayan da ta babbaka mijinta da tafasasshen ruwa, lamarin da ya yi wa mijin nata mummunan rauni a baya.

Sanarwar manema labarai da Jami’in Hulɗa da Jama’a na ‘yansandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi ya fitar a Abeokuta a ranar Lahadi, ta nuna Bisola ta faɗa a komar hukumar ce ranar 8 ga Maris biyo bayan rahoton da magidanta mai suna Peter Philip, ya kai a ofishin ‘yansandan na yankin Sango Ota.

Peter ya shaida wa ‘yansandan cewa matarsa na zarginsa da yawan shan giya sakamakon haka sai ta ɗauko wata tukunya ɗauke da tafasasshen ruwa ta kwara masa.

Isar batun gaban ‘yansanda ke da wuya sai Kwamandan ‘Yansanda na shiyyar, ACP Muhideen Obe ya bada umarnin a kamo matar da ta aikata wannan ɗanyen aiki.

Da take amsa tambayoyin ‘yansanda, Bisola ta bayyana wa jami’an cewa galibi maigidanta a buge yake dawo mata gida ba tare da taɓuka komai ba wajen kula da ɗawainiyarta da ta ‘ya’yansu.

Ta ci gaba da cewa a ranar da lamarin ya faru a buge ya shigo gida kamar yadda ya saba, sa’ilin da take yi masa ƙorafi game da mummunan halin shaye-shayen da yake yi sai ya haɗa da ita da iyayenta ya yi musu tatas da zagi wanda hankan ya fusata ta har ta kai ga ta kwara masa ruwan zafi.

A matakin farko binciken ‘yansanda ya gano cewa Bisola ta haihu kimanin watanni takwas da suka gabata, amma sai ta kashe abin da ta haifa saboda takaici tare da binne shi cikin sirri.

Tuni ‘yansandan suka tisa ƙeyar matar har zuwa inda ta binne abin da ta haifa. Yayin da shi kuwa maigidanta, an kai shi babbar asibitin Ota inda a yanzu haka ake ci gaba da ba shi kulawa.

Kwamishinan ‘Yansandan Jihar, CP Edward Awolowo Ajogun, ya bada odar a hanzarta miƙa batun ga sashen binciken manyan laifuka domin zurfafa bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *