‘Operation Lafiya Dole’ ta nemi haɗin kan ‘yan jarida

Daga FATUHU MUSTAPHA

Kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole, Major-General Faruk Yahaya, ya yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su mara wa jami’an tsaro baya domin kawo ƙarshen Boko Haram a Nijeriya.

Kwamandan ya yi wannan kira ne yayin wani taron karramawa da aka shirya wa ‘yan jarida a Barno a barikin sojoji da ke Maimalari a jihar.

General Yahaya ya nuna yabo tare da jinjina ga ‘yan jarida inda ya bayyana su a matsayin masu taka muhimmiyar rawa a fagen yaƙi da ta’addanci da ake ci gaba da fafatawa.

Ya ci gaba da cewa kafafen yaɗa labarai na da muhimmiyar gudunmawar da za su bai wa sha’anin yaƙi da matsalolin tsaro muddin kafafen za su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Daga nan ya buƙaci ‘yan jarida da kada su bari bango ya tsage balle ƙadangare ya samu wurin shiga game da yaƙi da muggan laifuka da ake yi a wannan ƙasa musamman kuma a yankin Arewa-maso-gabas.

Yahaya ya buƙaci a samu wata kyakkyawar alaƙa a tsakanin rundunar Operation Lafiya Dole da ‘yan jarida don kyakkyawar fahimta wajen gudanar da harkokin ɓangarorin biyu.

Taron ya samu halarcin ‘yan jarida daga ciki da wajen jihar Barno, ciki har da wakilan Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ) da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *