Ortom ya nemi Bala ya bai wa ‘yan ƙasa haƙuri kan furucinsa

Daga AISHA ASAS

Gwamnan Jihar Binuwai, Samuel Ortom, ya buƙaci takwararnsa na jihar Bauchi, Bala Mohammed, da ya fito ya bai wa ‘yan Nijeriya haƙuri game da furucin da ya yi na goyon bayan Fulani makiyaya su riƙa amfani da bindiga wajen kare kansu.

Ortom ya buƙaci haka ne yayin taron manema labarai da ya gudana a Makurdi a Litinin da ta gabata inda ya ce akwai buƙatar Gwamna Bala ya bada haƙuri domin sanyaya zukatan waɗanda suka rasa ‘yan’uwa sakamakon ayyukan ɓatagarin Fulani makiyaya.

Kazalika, Ortom ya buƙaci Gwamna Bala da ya yi koyi da takwarorinsa na Kano da Kaduna waɗanda su ma asalin Fulani ne, yadda suka nuna rashin jin daɗinsu dangane da ayyukan ɓatagarin makiyaya a jihohinsu.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar 12 ga Fabrairun 2021, an ji Gwamna Bala ya bada dalilan da suka sanya shi ganin dacewar makiyaya su riƙa amfani da bindiga wajen kare kansu.

Kodayake dai, Gwamna Bala ya ce furucin da ya yi na cewa makiyaya su yi amfani da bindiga wajen kare kai, al’amari ne na azancin magana wanda ke nuna tsantsar damuwa kan abin da ke faruwa, amma ba haƙiƙanin ɗaukar bindiga yake nufi ba. Kamar dai yadda ya shaida wa tashar Channels a Juma’ar da ta gabata.