Osinbajo da Sanwo-Olu sun ƙaddamar da kamfanonin ƙunzugun jarirai da audugar mata

Daga AMINA YUSUF ALI

A ranar Juma’ar da ta gabata ne, Mataimakin Shugaban Nijeriya, Farfesa Yemi Osinbajo da kuma Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu suka ƙaddamar da buɗe kamfanonin ƙunzugun mata da jarirai wanda aka yi a kan Dalar Amurka Miliyan $100.

Wato sun ƙaddamar da  ƙunzugun jarirai na babban kamfanin Huggies, sannan kuma audugar mata ta kamfanin Kotqex, waɗanda aka gudanar a yankin Odogunyan dake Ikorodu, a jihar Legas.

Sabon kamfanin wanda kamfanin Kimberly-Clark Nigeria, a filoti mai faɗin, 86,000m², an fara shi ne a cikin watanni 4 na ƙarshen shekarar da ta gabata, 2021. Amma matsalar dokar annobar Korona ta sa an ɗage ƙaddamar da kamfanin sakamakon dokar hana yin tarurruka da cinkoso. 

Mista Osinbajo ya bayyana cewa, an samar da wannan kamfani ne domin a rage ƙarancin samun kamfanonin na cikin gida da babu su sosai a  Nijeriya. Inda ya ƙara da cewa, a yanzu kamfanin Kimberly-Clark na Afirka ta Yamma ya tashi daga mai zuba hannun jari kawai a kamfanonin Nijeriya. Yanzu ya zama abokin kasuwanci a ƙasar wanda kuma ake sa ran zai ba da gagarumar gudunmowa wajen cigabanta. 

Shi ma a nasa jawabin, Gwamnan jihar Legas ya bayana irin farincikinsa da irin wannan karramawa da aka yi wa yankin Ikorodu. Don haka a cewarsa, wannan ƙalubale ne a gare su da su tabbatar da sun ƙara inganta yankin na domin ƙara samar da yanayi mai daɗi don samun nutsuwar masu zuba jari a yankin don su cigaba kawo wa yankin taimakon alkhairi. Inji shi.

Daga ƙarshe, Gwamnan ya taya kamfanin Kimberly-Clark a kan wannan ci gaba da ya samu. Sannnan ya ce Gwamanatinsa a shirye take don ganin ta ci gaba da ba da dama ga dukkan ‘yan kasuwa masu nufin zuba jarin a jihar Legas. 

Wasu manyan baƙi da suka samu halartar taron ƙaddamar da kamfanin, sun haɗa da Ministan masana’antu na Nijeriya da kasuwanci na Nijeriya, Richard Adebayo; sai qaramin ministan kuɗi da Kasafi, Clem Agba; Ministar harkokin mata, Pauline Tallen; Ɗan Majalisa mai wakiltar yankin Ikorodu, Babajimi Benson; Shugaban ƙungiyar masu ƙere-ƙere, a Nijeriya,  Mansur Ahmed; Mamallakiyar, American Business Council, Margaret Olele, da sauransu. 

Da ma wannan kamfani rahotanni sun nuna cewa, ya sha taka rawar gani wajen kawo abubuwan cigaba kamar ba da tallafin karatu da sauran abubuwa na cigaban mutane.