Osinbajo ya nemi maye gurbin shaidar zama ɗan jiha da ta haihuwa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi kira da a samar da kyakkyawar fahimtar juna a tsakanin masu faɗa aji, inda ya buƙaci a aiwatar da tsarin da zai inganta haɗin kan al’umma da haɗin kai a Nijeriya.

Osinbajo ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin ɗin da ta gabata a wajen taron ba da lacca mai taken ‘Policy Making and Good Governance Lecture Series’ wanda Cibiyar Nazarin Dabaru ta Ƙasa (NIPPS) ta shirya.

Yayin da ya ke magana kan batutuwan da suka shafi ƙaura, mataimakin shugaban ƙasar ya yi kira da a maye gurbin takardar shaidar zama ɗan jiha da ta haihuwa, yana mai jaddada cewa irin wannan matakin zai inganta haɗin kai.

Osinbajo ya kuma yi kira da a samar da tsarin shari’a mai ƙarfi da adalci wanda zai yi wa ’yan Nijeriya adalci ba tare da la’akari da ƙabilanci ko addini ba.

Mataimakin Shugaban Ƙasan ya kuma yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su sassauta batutuwan da suka shafi kabilanci da addini inda ya buƙace su da su riƙa yaɗa labaran da za su haɗa kan ’yan Nijeriya.

Mataimakin shugaban ƙasar, a cikin laccarsa mai taken ‘Ƙirƙirar Gida ga kowa: Gina Ƙasa a dimokuraɗiyya’, ya yi tir da yadda ake ta samun rarrabuwar kawuna, wanda a cewarsa, ke jawo koma bayan Nijeriya.

Ya ci gaba da cewa, “yawan ƙabilunmu ya kamata ya zama albarka ba la’ana ba,” ya ƙara da cewa Nijeriya na da damar zama babbar ƙasa.

Osinbajo, wanda ya bada misali da ƙasashen Singapore, Tanzania da Rwanda a matsayin ƙasashen da suka gudanar da harkokinsu yadda ya kamata, ya ce Nijeriya za ta iya ɗaukar darasi daga gare su.

“Yawancin ƙasashe daban-daban sun iya sarrafa da kuma amfani da nau’o’in su don amfanin kowa kuma mu ma za mu iya yin hakan a Nijeriya. Bambamcin mu a Najeriya bai kamata ya zama matsala ba.

” A gaskiya abin alheri ne, don haka dole ne mu bunƙasa ƙarfin sarrafa wannan bambancin domin cigaban al’ummarmu,” in ji Osinbajo.

Ya ƙara da cewa, “Don haka ya zama wajibi manyan masu faɗa aji su haɗa kai su amince a kawo ƙarshen matsalar ƙabilanci da addini da muke fama da su a halin yanzu a cikin al’ummarmu. Dole ne mu ba da fifiko ga abubuwan da suka haɗa mu tare da kuma lura da abubuwan da ka iya raba mu.”

Osinbajo ya yi imanin cewa, “‘yan siyasa da shugabannin al’ummar ƙasar za su iya taka rawa sosai wajen bunƙasa manufofi, dokoki da tabbatar da su wajen magance maƙamin ƙabilanci da addini a cikin al’ummarmu.”