Daga AMINA YUSUF ALI
Mataimakin shugaban ƙasar Nijeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya yi wasan vuya da Asiwsju Bola Ahmad Tinubu a daren ranar Asabar ɗin da ta gabata. Wato cikin dabara ya ƙi amsa gayyatar taron buɗe bakin azumin da Matar Shugaban ƙasa A’isha Buhari ta gayyace su. Saboda gudun haɗuwa da Tinubu.
Tinubu, da Dave Umahi da Chris Ngige, da sauran ‘yan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC sun halarci taron wanda ‘yan takarar PDP, Atiku Abubakar, Peter Obi da Bukola Saraki suka yi buris da shi. Kodayake, Gwamnan Bauchi, Bala Muhammad shi ya kawar da gabar ya halarci taron duk da cewa shi ɗan PDP ne.
Kodayake, Osinbajo ya samu wakilcin tsohon Gwamnan jihar Edo, Farfesa Oserheimen Osunbor, wanda shi ma lauya ne ɗanuwansa.
Amma da ya halarci taron da Kansa, da wannan taro zai kasance karo na farko da Osinbajo da Tinubu za su yi arba da juna tun bayan da kowanne su ya fito da matarsa a fili kuma ya ja tunga a kan takarar shugabancin Nijeriya tun a 11 ga watan Afrilun shekarar da muke ciki.
Alaqarsu ta ƙara danƙo sosai ne a lokacin da Osinbajo ya taɓa riƙe muqamin Kwamishinan Shari’a da kuma Antoni janar na tsahon shekaru takwas a Legas a lokacin da Tinubu yake Gwamnan jihar tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007.
Rahotanni sun bayyana cewa, Osinbajo yana jihar Oyo a garin Ibadan ranar Juma’a wato jajiberin ranar taron. Amma dai har yanzu ba a san meye dalilin da ya hana shi keta hazo ya dawo zuwa Abuja ba ranar Asabar don halartar taron na Uwargidan Shugaban ƙasa ba.
A taron ne dai A’isha Buhari take roƙon ‘yan takarar da su sanya mata a matsayin abokan takarar tasu.
A wajen taron ne dai Osinbajo ya aiko da saƙo na jawabi wanda wakilinsa Osunbor ya karanta a zauren taron, wanda yake kira ga sauran ‘yan takara ‘yanuwansa da su yi siyasa ba da gaba ba. A Inda ya ƙara da cewa, taron zai ba da dama a samu haɗin kai tsakanin ‘yan Nijeriya da suka fito daga asali da kuma addinai mabanbanta.
Kuma ya ƙara da cewa, ya kamata ‘yan takara su sani, ita wannan takara ba ta ko a mutu ko a yi rai ba ce. Dole a ƙarshe dai mutum guda shi zai ka da sauran ya lashe zaben da za a yi shekara mai zuwa. Don haka a cewar sa, ya kamata sauran su ɗauki matakin yin siyasa ba da gaba ba.
Har yanzu dai akwai rarrabuwar ra’ayi tsakanin ‘yan Nijeriya a kan ko ya kamata Osinbajo ya haɗa takara da ubangidansa, Bola Tinubu, ko bai kamata ba.