Oyebanji ya lashe zaɓen Ekiti

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta tabbatar da Mr. Biodun Oyebanji na Jam’iyyar APC, a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna a Jihar Ekiti da ya gudana a ranar Asabar da ta gabata a jihar.

Mr Oyebanji ya lashe zaɓen ne bayan da ya samu ƙuri’a 187,057, inda ya kayar da abokan hamayyarsa Segun Oni na SDP da Bisi Kolawole na PDP da sauransu.

Jam’iyyar SDP ce ta zo ta biyu a zaɓen da ƙuri’u 82,211, yayin da PDP ta zo ta uku da ƙuri’u 67,457.

Ya zuwa watan Oktoba mai zuwa ake sa ran za a rantsar da Mr Oyebanji a matsayin sabon gwamnan Ekiti don ya gaji mai barin gado Kayode Fayemi.