Oyo: Makinde ya rufe kasuwar Shasha saboda ɓarkewar rikici

Makinde

Gwamman jihar Oyo, Engr. Seyi Makinde, ya bada umarnin rufe kasuwar Shasha da ke Ibadan har sai abin da Allah Ya yi biyo bayan ɓarkewar rikici a tsakanin ‘yan kasuwan kasuwar.

Kazalika, gwamnan ya sanya dokar taƙaita zirga-zirga a ciki da kewayen ƙaramar hukumar Akinyele sakamakon zaman ɗar-ɗar da jama’a ke yi a yankin da kasuwar take. Duka wannan ya faru ne a ranar Asabar, 13/02/2021.

Sanarwar da ta fito daga ofishin Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnatin Jihar, Mr. Taiwo Adisa, ta nuna Gwamna Makinde ya ɗauki wannan mataki ne domin lafar da ƙurar da hargitsin ya tayar.

Sakataren ya ce dokar taƙaita zirga-zirgar za ta riƙa aiki ne daga ƙarfe 6 na yamma zuwa 7 na safe.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*