PAPSS zai rage buƙatar amfani da Dala da Fam a Afirka – Emefiele

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, CBN, Godwin Emefiele ya bayyana cewa, dandalin hada-hadar kuɗi tsakanin ƙasashen Afirka, PAPSS, zai kawo ƙarancin buƙatar amfani da kuɗaɗen waje a yayin cinikayya tsakanin ƙasashen Afirka.

Wato tasirin Dala da Fam har ma da Yuro zai ragu matuqa a yankin na Afirka. 

Gwamnan ya yi wannn bayani ne a yayin ƙaddamar da dandalin na PAPSS a garin Accra na ƙasar Ghana a ranar Larabar makon da ya gabata.

Bankin safarar kayayyaki na ciki da wajen Afirka, da Bankin Afrexim, tare da haxin gwiwar Cibiyar haɗin kan Afirka (AU) hukumar AfCFTA, su ne suka ƙaddamar da wannan shiri na PAPSS domin ɗabbaƙa kasuwanci a tsakanin ƙasashen.

Kafin ƙaddamar da tsarin PAPSS ɗin, ƙasashen Afirka kan yi asarar kusan Dalar Amurka biliyan biyar kowacce shekara. Domin kafin a ƙulla kowacce irin cinikayya a tsakanin ƙasashen na Afirka ana buƙatar canjin kuɗin ƙasar waje da kuma amfani da wani banki da ba na Afirkan ba. 

A don haka a cewar sa, ƙaddamar da tsarin zai ƙara samar da damammaki ga ‘yan Afirka kuma ya ƙara bunƙasa kasuwanci tsakanin ƙasashensu.