PDP 2023: Baki ya zo ɗaya a tsakanin ‘yan takarar shugabancin Nijeriya

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike a ranar Laraba da ta gabata ne tare da sauran masu neman tsayawa takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP suka yi wata ganawar sirri a tsakanin su a gidan gwamnatin Ribas dake garin Fatakwal.

Waɗanda suka halarci ganawar sun haɗa da Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, takwaran sa na Jihar Sakkwato, Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal, da tsohon shugaban Majalisar Dattawa ta Nijeriya, Dokta Abubakar Bukola Saraki, da kuma tsohon shugaban bankin FSB International Bank, Dokta Mohammed Hayatu-Deen.

Da yake yi wa manema larabai jawabi jin kaɗan bayan kammala zaman nasu, Gwamna Wike ya bayyana cewar, manufar su ita ce a samu haɗin kai a cikin jam’iyyar ta su ta PDP.

Gwamnan na Jihar Ribas ya kuma bayyana cewar, ɗaukacin masu neman tsayawa takarar shugabancin suna kuma son daɗaɗa wa ‘yan Nijeriya ta hanyar ganin cewar, sun kawo wani kyakkyawan tsari da zai sanya jam’iyyar PDP ta lashe zaɓen shugaban ƙasa, a kakar shekarar zaɓe ta baɗi, 2023.

Ya ce, “babban abin sha’awar mu shine a samu haɗin kai a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar mu da zummar tabbatar da ganin jam’iyyar PDP ta riƙe madafun mulkin ƙasar nan a shekara ta baɗi idan Mai Duka ya kai mu, domin ‘yan Nijeriya sun himmatu da kasancewar ganin hakan. Ina baku tabbaci na cewar, za mu dunƙule mu zama abu guda domin faranta wa ‘yan Nijeriya.”

Shi ma da yake tsokaci, tsohon shugaban Majalisar Dattawa ta Nijeriya, Dokta Abubakar Bukola Saraki ya bayyana cewar, suna tattaunawa ne domin zaƙulo bakin zare na samar da ingantacciyar madafa ta haɗin kai a tsakanin su da kuma ɗaukacin ‘ya’yan jam’iyyar.

Saraki ya ce, “muna da masaniyar cewa ‘yan Nijeriya sun zuba wa jam’iyyar PDP idanuwan su a matsayin ita ce ginshiƙi ɗaya ƙwal da za ta samar wa ƙasar mafita daga cikin ɗimbin ƙalubaloli da suka yi mata katutu.

“Mun hallara ne a nan domin tattaunawa, kuma mun kammala zantattukan mu dangane da yadda za mu ƙarfafa haɗin kai a cikin jam’iyyar mu, mu tabbatar bakuna sun kasance bai ɗaya ta yadda za mu samar wa ƙasar ingantaccen jagoranci.

“Mun fahimci alfanun yin haka, kuma PDP ita ce kaɗai madafar da za ta samar mana mafita, wanzar da cigaba da haskaka dukkan lamarorin mu.

“Ya baje mana dukkan ra’ayoyin sa na siyasa, tare da bayar da ingantattun shawarwari waɗanda za mu cigaba dayin amfani dasu, amma muhimmin lamari shine na haɗin kai a tsakaninn mu, domin jam’iyya ta zarce gaban burace-buracen mu, abu mafi muhimmanci shine haɗin kai, kishin ƙasa ya zarce duk wani son zuciya na ɗaiɗaikun mu, ƙasa ce akan gaba,” inji Saraki.