PDP a Zamfara ta ƙaryata rahoton dakatar da Shugaban Jam’iyya

Daga SUNUSI MUHAMMAD a GUSAU

Babbar jam’iyyar hamayya ta PDP a Jihar Zamfara ta ƙaryata rahotannin dake yawo a kafofin watsa labarai cewa, kwamitin zartarwa na jam’iyyar ya dakatar da shugaban jam’iyyar na jihar, Kanal Bala Mande (Mai ritaya).

Sakataren yaɗa labarai na Jihar, Abba Bello Ouando ne ya sanar da haka ga manema labarai a wajen taron manema labarai a Gusau ranar Alhamis da ta gabata.

Abba Bello ya ce, yana Abuja lokacin da ya ga wata wasiƙa na karakain kafofin watsa labarai da sada zumunta wadda ya sanya wa hannu cewa PDP a Jihar Zamfara ta Dakar da shugaban sam’iyyar na jihar bisa zargin zagon ƙasa.

Abba Bello ya ƙara da cewar, babu ƙamshin gaskiya a lamarin kuma ba shi ne ya sa hannu a takardar ba.

A nasa tsokacin, mataimakin shugaban Jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara, Farfesa Bashir Jabaka, ya zargi jam’iyyar adawa da kitsa makircin don su tarwatsa Jam’iyyar ta PDP a Jihar Zamfara.

“Muna da tabbacin cewar, jam’iyyar adawa ce ta shirya wannan makircin kuma za mu ɗauki matakin tabbatar da hakan bai sake faruwa ba,” inji shi.

Daga nan, ya yi kira ga dukkan magoya bayan Jam’iyyar PDP a jihar da su yi fatali da rahoton dakatarwar saboda ba gaskiya ba ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *