PDP da LP suna shirya manaƙisa don hana rantsar da ni a matsayin shugaban ƙasa – Tinubu

Daga AMINA YUSUF ALI

Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Nijeriya, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya kwarmata irin makircin da ya ce wasu fusatattun ‘yan siyasa suke shirya masa don kawo cikas ga rantsar da shi a matsayin sabon shugaban Nijeriya a ranar 29 ga Mayun 2023.

Tinubu ya yi wannan ikirarin ne a wani jawabi da Daraktansa na hulɗa da jama’a kuma Ministan ƙwadago da ba da aiki Mista Festus Keyamo SAN ya wallafa ranar Asabar 25 ga watan Maris, 2023, a Abuja.

Jawabin ya yi gargaɗi ga ‘yan takarar shugabancin Nijeriya na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, da na jam’iyyar LP, Mista Peter Obi da su daina yawo a tituna alhali sun miƙa buqatar neman haƙƙoƙinsu a kotu.

Wani ɓangare a cikin jawabin ya bayyana cewa: ” Muna sane cikin damuwa a kan wasu halaye na Allah wadai da wasu mutane da wasu mutane da wasu gungu suke yi waɗanda suka sha alwashin kawo cikas ga demokraɗiyya”.

Saboda wasu dalilai nasu da su kaɗai suka sani, waɗannan mutane sun kasance cikin adawa da kasancewar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a shekarar 2023. Waɗannan mutane masu son zuciya sun dage sai ko dai sun soke sakamakon zaɓen ko kuma sun hana rantsar da shugaban ƙasa a ranar 29 ga Mayu, 2023″.

A cewar jawabin dai, Tinubu ya bayyana cewa, wannan matsaya tasu da ma ta saɓa da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin ƙasar nan na dokokin zaɓe. Hakazalika, saboda da illar abin ga zaman lafiya da tsaron ƙasa, muka ga ya zama dole mu jawo hankalinsu”. Inji shi.

Ya ƙara da cewa, suna sane da masu yin wasu al’amura na cin amanar qasa, sannan suna sane da masu shirya makirci don yi wa demokraɗiyya zagon ƙasa. Wasu sun riga sun shirya manaƙisa da sojoji su ƙwace ƙasar, alhali sun tava yi kuma bai haifar wa ƙasar ɗa mai ido ba. Sannan suna kan ingiza mutane don yin adawa da gwamnati mai hawa gado.

Kuma a cewar sa, idan manufarsu su hana rantsar da sabon shugaban ƙasa da mataimakinsa ne, ya kamata su canza tunani. Domin a yanzu haka shugaban ƙasa ya riga ya tsara matakan yadda za a miƙa mulki a tsare. Don haka, miƙa mulki ga sabon shugaban ƙasa ba zai zama abun ce-ce-ku-ce ba.

Kuma a cewar sa, tun bayan lashe zaɓensa a matsayin shugaban ƙasa, jawabansa da furucinsa kullum sun kasance na neman sulhu da yafiya da kuma fatan alkhairi ga Nijeriya ne.

Kuma zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya ce yana sane da waɗanda suke ɗaukar nauyin ta da tarzoma a ciki da wajen Nijeriya kuma zai cigaba da aiki kusa-da-kusa da jamian tsaro don tabbatar da an gurfanar da su gaban kuliya.

Bayan an bayyana su a matsayin waɗanda suka gi nasara, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Sanata Kashim Shettima suna da haƙƙin rantsar da su don su kama ayyukansu, saboda shi ne abinda aka saba tun shekarar 1999, daga nan kuma waɗanda suke da taƙaddama sai su je kotuna don bin kadinsu. Amma me ya banbanta wannan zave da na 1999?

Don haka a cewarsa, ya kamata waɗanda suka faɗi zaɓe su kama kansu cikin mutunci, Nijeriya ba ƙasa ce marar doka ba, bai kamata a cewar sa wasu da suka sha kaye su dinga nuna hakan ba. Sun ɓige da yaɗa farfaganda da labarun ƙarya, da cin mutunci da ɓatanci a kafafen yaɗa labarai.

A cewar sa, burinsa shi dai kawai ganin zaman lafiya ya wanzu a ƙasar nan, kuma suna sane da waɗanda suke ɗaukar nauyin ta da wancan hargitsi, kuma da sannu za a gurfanar da su a gaban hukuma.