PDP ta ƙaryata labarin dakatar da shugabanta na ƙasa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Da sanyin safiyar yau ne wasu labarai marasa tushe suka taso a kafafen sada zumunta na zamani waɗanda ke nuna cewa an dakatar da shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu bisa zargin karkatar da dukiyar jama’a, inda aka naxa Mataimakinsa na Arewa, Ambasada Umar Damagun a matsayinsa.

A wata sanarwar da Shugaban Sadarwa da Dabaru na Jam’iyyar na ƙasa, Simon Imobo-Tswam ya fitar kuma ya raba wa manema labarai a ranar Laraba, ya ce, “ko da ya ke ba ma so mu amsawa labarin ƙarya, amma dole mu mayar da martani don dakatar da ci gaba da yaxa wannan jita-jitar.

Ya qara da cewa, “har yanzu Dakta Iyorchia Ayu, shi ne Shugaban PDP na ƙasa. Ayu ya ɗauki hutun sati biyu da ya cancanta a ranar 21 ga watan Yuni, 2022. Zai dawo mako mai zuwa domin ci gaba da aiki, wanda mu ke sa ran sai zama ranar 6 ga Yuli, 2022.”

“Ayu ya miƙa a hukumance ga mataimakinsa (Arewa), Ambasada Umar Damagun. Kuma mataimakin na sa ya fara aiki tun daga wannan rana,” inji sanarwar.

Ya ce, “a bisa wannan mukami ne shi Damagun ya jagoranci taron ƙaddamar da majalisar yaƙin neman zaɓen gwamnan jihar Osun, ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Bayelsa, H.E. Douye Diri.”

“Idan ba da wata niyya masu shafukan Facebook su ke irin wannan abu ba, da sun ji lokacin da shugaban riƙo na ƙasa, Amb. Damagun, a yayin bikin ya ke cewa, a madadin shugabana na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu, na ƙaddamar da wannan taro.

“Don haka ana shawartar jama’a da su yi biris da miyagun labaran da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta na zamani, domin kuwa aikin ɓarna ne kawai, kuma ayyukan banza ne,” inji sanarwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *